An samu gobara a Kotun Kolin Najeriya da ke Abuja a safiyar Litinin.
Gobarar ta babbake ofisoshin wasu alkalai uku, a yayin da ma’aikata suka tsere domin kubutar da rayuwarsu.
- A wata 4 Tinubu ya ciwo bashin tiriliyan 1.6 daga Bankin Duniya
- NAJERIYA A YAU: “Yadda Na Sayar Da Kayan Gadona Na Yi Karatu”
Zuwa yanzu dai ba a kai ga gano musabbabin tashin gobarar ba, amma majiyarmu ta ce jami’an hukumar kashe gobara sun isa harabar kotun.
Wannan na daga cikin gobarar da aka samu a manyan cibiyoyin gwamnati a Babban Birnin Tarayya, Abuja.
A watan Mayun 2023 gobara ta lakume wani yanki na barikin sojojin sama da ke Abuja.
A cikin watan ne aka yi gobara a ginin Hukumar Akwatin Gidan Waya (NIPOST) a Abujar.
A watan Afrilu Ofishin Akanta-Janar na Kasa (AGF) ya yi gobara.