✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Gobara ta tashi a kasuwar kayan mota ta Ladipo

Gobarar ta lakume wani babban bene da ake sayar da kayayyakin mota.

Gobara ta tashi a sananiyar kasuwar sayar da kayayyakin mota ta Ladipo da ke Jihar Legas da sanyin safiyar Lahadi.

Gobarar ta lakume wani bene mai hawa daya da ake sayar da kayayyakin mota a kasuwar.

“Hukumar Agaji ta Jihar Legas (LASEMA) da Hukumar Kashe Gobara ta Jihar Legas da Hukumar Kashe Gobara ta Tarayya  sun yi kokarin dakile yaduwar gobarar zuwa wasu gine-gine,” a cewar Shugaban LASEMA, Olufemi Oke-Osanyintolu.

Sai dai zuwa yanzu hukumomin kashe gobara a jihar ba su bayyana dalilin tashinta ba.

Hukumar LASEMA ta ce an samu nasarar kashe wutar kuma ana ci gaba da samun ruwan da ake kashe ta.