✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Gobara Ta Tashi A Kasuwar Bayan Tasha Da Ke Damaturu

Wata shu'umar gobara ta tashi a Kasuwar Bayan Tasha da ke garin Damaturu a Jihar Yobe

Wata shu’umar gobara da ta tashi a Kasuwar Bayan Tasha da ke garin Damaturu, fadar Jihar Yobe ta barnata shaguna da dukiyoyi na milyoyin Naira.

Wani ganau ya shaida wa Aminiya cewa gobara ta tashi ne da misalin karfe 1.00am na dare, kafin wayewar ranar Talata, inda ta kona shaguna sama da 20 cike da kayayyaki akasari irin na mata.

Ana zargin wutar lantarki ce ta haddasa wannan gobara wadda ta faro daga shagon wani mai sayar da hijabai.

Bayan da tashin gobarar ne wata tukunyar iskar gas ta fashe, lamarin da ya watsa wutar zuwa wasu shaguna da ke kasuwar da ke kusa da Masallacin Jumu’a na JIBWIS.

Wani jami’in hukumar ya shaida wa wakilinmu cewa, an kashe gobarar ne bayan da suka shiga wurin a kan lokaci sakamakon wani kira na gaggawa da suka samu wadda ba su yi wani jinkiri ba suka garzaya domin kauce wa asarar rayuka da dukiya.

Wannan dai ba shi ne karon farko ba da ake samun tashin gobara a kasuwar, wadda lokaci zuwa lokaci a kan samu faruwar irin wannan iftila’i, wanda wasu ke alakantawa da sakacin wasu ’yan kasuwar da ke barin kayayyakin da ke amfani da wutar lantarki a kunnen bayan sun tashi daga kasuwar.

Wasu kuma na alakanta gobarar da cinkoso a kasuwar wanda masu ra’ayin hakan suk ce na haifar da yawaitar tashin gobara.

Wasu kuma na ganin cewar, da gwamnatin Jihar Yobe za ta kokarta wajen bude sabuwar kasuwar da tuni aka kammala ta, tare da tilastawa ‘yan kasuwar komawa cikinta, to da an rage yawaitar tashin gobarar.