✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Kano Poly ta yi Gobara

Gobarar ta kone daukacin sashen al'adu da masana'antu na kwalejin.

Gobara ta tashi a Kwalejin Kimiyya da Kere-kere ta Jihar Kano (Kano Poly) a safiyar  ranar talata.

Hukumar Kashe Gobara ta Jihar Kano ta sanar cewa gobarar ta kone daukacin sashen al’adu da masana’antu na kwalejin.

Kakakin hukumar, Saminu Abdullahi, ya ce kawo yanzu ba a kai ga gano musabbabin tashin gobarar ko girman barnar da ta yi ba.

Saminu Abdullahi ya kara da cewa mhaukunta na ci gaba da gudanar da bincike a kan lamarin domin gano hakikanin abin da ya faru.