✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Gobara ta tashi a Hedkwatar Tsaron Najeriya

Ba a kai ga gano musabbabin gobarar ba

Wata gobara ta tashi a hawa na biyu na ginin Hedkwatar Tsaron Najeriya da ke Abuja da tsakar ranar Litinin.

Rahotanni sun ce ba a kai ga gano musabbabin gobarar ba, har zuwa lokacin hada wannan rahoton.

Daraktan Yada Labarai na Hedkwatar, Manjo-Janar Jimmy Akpor, wanda ya tabbatar da faruwar lamarin ya ce saun sami nasarar kashe ta.

Ya ce hadakar jami’an Hukumar Kashe Gobara ta Tarayya da na sojoji ne suka kashe wutar.

Jimmy ya ce, “Cikin ikon Allah yanzu komai ya daidaita. Tuni kuma aka fara gudanar da bincike da nufin gano musabbabin tashin wutar.

“Muna godiya ga jami’an Hukumar Kashe Gobara ta Tarayya da ilahirin jama’a saboda ci gaba da bayar da hadin kai da goyon bayan da suke ba sojojin Najeriya,” inji shi.