Hediwatar Hukumar Zabe ta Kasa (INEC), reshen Jihar Enugu ta kama da wuta a daren ranar Lahadi.
Ofishin ya kama da wuta ne mako guda bayan gobara a ofishin INEC na Karamar Hukumar Udenu ta Jihar.
- Ofishin INEC ya kama da gobara
- NECO ta saki sakamakon jarabawar 2020
- ’Yan bindiga sun sako Daliban Afaka
- Mayakan Boko Haram sun kai hari Bauchi
Kwamishinan ’yan sandan Jihar, Mohammed Aliyu, ya tabbatar ta tashin gobarar a ofishin da ke unguwar Achi, daura da Bankin Manoma, a Enugu.
Kwamishinan ’yan sandan ya ce yana wajen da gobarar ta shi don ba da dauki, amma bai amsa ragowar tambayoyin da aka masa ba.
Daga bisani an hangi Hukumar Kashe Gobara ta Tarayya, da ta Jihar Enugu na kai komo wajen ganin sun kashe wutar.
Kokarinmu na jin da bakin kakakin INEC na Jihar Enugu, Dokta Emeka Ononamadu, bai cimma nasara ba, domin bai amsa kiran wayar da aka masa a lokacin da wutar ke tsaka ci ba.