✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Gobara ta tashi a dakin kwanan dalibai mata a Jami’ar Maiduguri

Gobarar ta tashi ne daga rishon girkin da daliban ke yi a dakin kwanansu.

Gobara ta tashi da dakin kwanan dalibai mata a Jami’ar Miduguri da ke Jihar Borno.

Hukumar gudanarwar Jami’ar Maiduguri ta tabbatar da aukuwar lamarin, tana mai bayyana cewa wutar ta tashi ne daga girkin da daliban suke yi a dakin kwanansu.

Sanarwar da Jami’in Hulda da Jama’a na Jami’ar Maiduguri, Farfesa Danjuma Gambo, ya fitar ta ce gobarar ta ci daki daya a daya daga cikin gine-ginen dakunan kwanan daliban, amma ba a samu rauni ba, ballantana asarar rai.

Farfesa Gambo ya bayyana cewa binciken farko-farko da aka gudanar ya nuna gobarar ta tashi ne daga rishon girkin daliban, amma za a gudanar da cikakken bincike.

Majiyarmu ta ce gobarar ta kama ne da misalin Azahar a daya daga dakunan kwanan daliban a ranar Alhamis kafin daga bisani jami’an kashe gobara su yi nasarar kashe ta.