✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Gobara ta laƙume kasuwar waya a Kogi

Mun yi asarar duk kayayyakinmu da a yanzu za a ɗauki lokaci kafin mu iya farfaɗowa.

Wata gobara da ta tashi da sanyin safiya ta laƙume dukiya ta miliyoyin naira a kasuwar wayar salula da ke Lokoja, babban birnin Jihar Kogi.

Aminiya ta ruwaito cewa gobara a kasuwar wadda ake kira GSM Village da ke zaman wani rukuni na Kasuwar Kpata a birnin Lokoja, ta tashi ne da misalin ƙarfe 5 na Asuba sakamakon tangarɗar da aka samu ta wutar lantarki a yankin.

’Yan kasuwa da dama sun bayyana cewa sun gaza kwashe dukiyarsu a yayin ibtila’in a sakamakon wutar da ta gagari kundila.

Daga cikin kayayyakin da gobarar ta laƙume haɗi da shaguna sun haɗa da wayoyin hannu, kwamfutoci, fankoko da sauran kayayyakin laturoni.

Wani ɗan kasuwar mai suna Stephen Ajebo, ya ce wani abokin kasuwancinsa ne ya sanar da shi faruwar ibtila’in da misalin ƙarfe 5:25 na safiya.

“Wani abokina ne ya kira ni da misalin ƙarfe 5:25 yana sanar da ni cewa gobara ta tashi a Kasuwar Salula.

“Ina zuwa na tarar shagona ya ƙone ƙurmus har da wayoyin kwastomomina da ke wurina.

Wata Madam Josephine Adejo da ke sayar da kayayyakin wayar salula a kasuwar, ta ce sun yi asarar duk kayayyakinsu da a yanzu za a ɗauki lokaci kafin su iya farfaɗowa.

A cewar sakataren harkokin kuɗi na ƙungiyar dilolin wayar salula a kasuwar, Moses Felix, ya ce ibtila’in ya taɓa shi ta kowane ɓangare.

“Sai da na yi kuka lokacin da shagona ya ƙone ƙurmus saboda babu abin da zan iya. Ina harkar kwamfutoci. Gaba ɗaya kayayyakin da na yi oda waɗanda aka kawo min a wannan makon sun ƙone ƙurmus.

“Mafi yawanmu mun kammala karatu, kuma muka kama wannan sana’a domin samun abin dogaro da kai. Akwai kimanin matasa 200 da ke wannan sana’a a yanzu.”

Bayanai sun ce gobarar ta gagari ’yan kwana-kwanan da suka ziyarci kasuwar da tun kafin zuwansu ta laƙume shaguna da dama.