Gobara ta lalata kadarori na miliyoyin Naira a kauyukan Malamawar Dangoli, Karangi, da Kwalele da ke Karamar Hukumar Kiyawa ta Jihar Jigawa.
Gobarar da ta auku a ranar Lahadi, ta lalata gidaje, dabbobi, kayayyakin gonada sauran dukiyoyi.
- Bayan shekara 10, Buni ya soke haramcin hawa babur a Gabashin Yobe
- Kanawa 10 ’yan uwan juna sun mutu a hatsarin mota a Kaduna
’Yan sanda da jami’an kashe gobara daga jahohi, tarayya da ta filin jirgin sun je wurin da lamarin ya faru domin kashe wutar.
Kakakin ’yan sandan, DSP Lawan Shiisu Adam, ya ce, “Kawo yanzu babu asarar rayuka, amma wasu har yanzu ba a san inda wasu da suka tsere domin kubutar da rayuwarsa suke ba.”
Daraktan Hukumar Kashe Gobara na jihar, Ibrahim Abdullahi Gumel, ya ce gobarar ta tashi ne sakamakon kona gona da wasu da ba a san ko su waye ba suka ajiye a kauyukan.
Ya yi kira ga jama’a da su daina kona ciyayi da busassun abubuwa a kauyuka a wannan yanayi da damina ke shirin faduwa.