✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Gobara ta lalata amfanin gonar miliyan 24 a Yobe

Ana zargin gobarar ta tashi ne sakamakon taba sigari da yar a wata gona

Gobara ta lalata amfanin gona da darajarsu ta kai Naira miliyan 24 a Karamar Hukumar Gulani da ke Jihar Yobe.

Jami’in Yada Labarai na karamar hukumar, Ali Abdullahi ne, ya bayyana hakan a wata hira da Kamfanin Dillacin Labarain Najeriya (NAN) a garin Gulani a ranar Alhamis.

Abdullahi, ya ce gobarar ta tashi ne ranar Talata da yamma, inda ta lalata gonakin gero 16 da ke da fadin kadada 115.

Kazalika, ya ce hukumomin yankin na zargin gobarar ta tashi ne sakamakon watar guntun taba sigari da aka yar a gefen wata gona.

“Yawanci lokacin girbi, iska tana kadawa sosai kuma idan makiyayan da ke kewayen yankin suka yar da sigari a kan ciyayi ko suka kunna wuta don kare shanunsu daga cizon kwari, cikin sauki wuta za ta iya tashi,” inji shi.

Abdullahi ya ce tuni Shugaban Karamar Hukumar Gulani, Dayyabu Jibilwa, ya kafa kwamiti don binciken irin asarar da aka yi.

Ya ce Jibilwa ya jajanta wa manoman da abin ya shafa, ya kuma ba su tabbacin cewa gwamnatin jihar da ta karamar hukumar za su tallafa musu don rage musu radadin asarar da suka tafka.