✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Gwamnatin Yobe na ciyar da almajirai a Tsangayu 85 kullum

Ya ce zuwa yanzu gwamnatin ta ɗinkawa almajirai 850 tufafin sawa.

Gwamnatin Jihar Yobe ta kafa cibiyoyin bayar da abinci 85 domin samar wa almajirai abinci a dukkanin Ƙananan Hukumomin 17 na jihar, a lokacin azumin Ramadan.

Sakataren zartarwa na Hukumar Ilimin Larabci da Addinin Musulunci ta Jihar Yobe, Malam Umar Abubakar ne, ya bayyana hakan a wata hira da Daily Trust a ranar Alhamis.

“Muna bai wa makarantun Tsangaya 85 kayan abinci 85, biyar a kowace Ƙaramar Hukuma, inda muke ciyar da almajirai tsakanin 300 zuwa 400 a kowace makaranta,” in ji shi.

Ya ƙara da cewa Gwamna Mai Mala Buni ne, ya amince da wannan shiri domin tallafa wa yara marasa galihu a jihar.

Baya ga haka, gwamnatin ta buɗe manyan cibiyoyin ciyarwa guda uku a Damaturu domin ciyar da sama da almajirai 2,000 da wasu mabuƙata.

Abubakar, ya bayyana cewa hukumar na kuma samar wa almajiran kayan sakawa.

“Mu na da alhakin tabbatar da cewa waɗannan yara sun ji cewa suna cikin al’umma.

“Zuwa yanzu mun ɗinkawa sama da 850 daga cikinsu tufafi, kuma Insha’Allah, muna da shirin ƙara wannan adadi a nan gaba,” in ji shi.

Ya gode wa gwamnan saboda goyon bayansa tare da kira ga sauran gwamnatoci da masu hali da su taimaka wajen tallafa wa yara marasa ƙarfi a cikin jama’a.