An samu tashin gobara a daren ranar Litinin a babbar kasuwar Kafanchan da ke karamar hukumar Jama’a a jihar Kaduna, gobarar ta lakume akalla dukiyar da ta kai Naira miliyan 1.5 a kasuwar.
Shugaban kungiyar ‘yan tireda na kasuwar Alhaji Salisu Idris ya bayyana wa majiyarmu cewa, gobarar ta cinye shaguna 14 wanda hakan babbar asara ce ga masu shagunan, kuma ya bukaci gwamnati da ta taimakawa ‘yan tiredan da suka yi asarar dukiyar su.
Shugaban karamar hukumar Peter Danjuma Averick, ya jajantawa wadanda suka yi asarar dukiyar su kuma ya yi alkawarin tallafa wa ‘yan tiredan.