✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Gobara ta lakume rumfunan kasuwa a Legas

Wasu ‘yan kasuwa a Legas sun wayi gari cikin alhini bayan gobara ta lakume rumfunansu da tarin dukiyoyinsu na miliyoyin Naira. Mun samu wannan rahoto…

Wasu ‘yan kasuwa a Legas sun wayi gari cikin alhini bayan gobara ta lakume rumfunansu da tarin dukiyoyinsu na miliyoyin Naira.

Mun samu wannan rahoto ne yayin da ‘yan kwana-kwana na kokarin kashe wutar da ta tashi da sanyin safiyar Asabar, 27 ga watan Yuni a shiyyar rukunin gidaje na Gowon a Legas.

Zuwa lokacin hada wannan rahoto ba a kai ga gano musababbin gobarar da ta lakume rumfar kasuwar guda 11 ba, lamarin da ya yi sanadiyar salwantar dukiyar miliyoyin Naira.