✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Gobara ta lakume rayuka biyu da gidaje 500 a Borno

An ba da umarnin gano musabbabin afkuwar gobarar tare da tabbatar da irin barnar da ta yi.

Akalla mutane biyu ne suka mutu sakamakon wata gobara da ta kone sama da gidaje 500 a garin Gajiganna da ke Karamar Hukumar Magumeri a Jihar Borno.

A rahoton da ya fito daga garin na Gajiganna ya nuna cewar, har ya zuwa yanzu dai ba a san musabbabin gobarar da ta afku a yammacin ranar Alhamis kamar yadda mazauna garin suka bayyana.

Shugaban Majalisar Karamar Hukumar ta Magumeri, Injinya Ali Yaumi, a jiya Juma’a ya kai ziyarar jajanta wa wadanda gobarar ta shafa da kuma duba irin barnar da ta yi da nufin taimakawa wadanda abin ya shafa.

Injiniya Yaumi ya lura cewa sama da gidaje 500 ne suka kone kurmus yayin da gobarar ta salwantar da rayuka biyu sannan wasu biyu suka samu munanan raunuka kuma a halin yanzu suna kwance a asibiti a garin Gajiganna.

Ya yi addu’ar Allah Ya jikan mamatan da kuma rokon Allah Ya kare afkuwar irin wannan lamarin nan gaba, tare da yin kira ga wadanda abin ya shafa da su rungumi lamarin a matsayin jarrabawa.

Shugaban ya kuma yaba da goyon baya da hadin kan al’umma, ya kuma yaba da irin namijin kokarin da rundunar sojojin Najeriya mai hedikwata a garin Gajiganna ke yi na maido da zaman lafiya a yankin da kewaye.

Sai dai ya bayar da umarnin gudanar da bincike cikin gaggawa kan afkuwar gobarar tare da tabbatar da irin barnar da gobarar ta yi.

Ya kuma yi alkawarin sanar da gwamnatin jihar abin da ya faru domin daukar matakin gaggawar kan wannan lamari musamman wajen kawo tallafi ga wadanda wannan iftila’in ya afkawa.

Kazalika, gwargwadon iko Injinya Yaumi ya tallafa wa wadanda abin ya shafa da wasu kudade don rage musu radadi.

Wakilinmu yaa ruwaito cewa, Injiniya Yaumi ya samu rakiyar mai bai wa gwamnan shawara na musamman Bukar Bussami da Sakataren Majalisar, Goni Kundube da Ali Lawan Kyari, Darakta  da  DPO na karamar hukumar  da sauran masu ruwa da tsaki a yankin.