✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Gobara ta lakume rayuka a kasuwar Abuja

Ana fargabar 'yan kasuwa da dama sun mutu a gobarar da tashi a kasuwar Maitama.

Gobara ta tashi a kasuwar Maitama da ke yankin Kubwa na Karamar Hukumar Bwarin ta Abuja, babban birnin Najeriya.

Bayanai sun ce wannan musiba ta auku ne da misalin da karfe bakwai na yammacin ranar Juma’a yayin da ake tsaka da rufe kasuwar.

Wata majiya  ta bayyana cewa gobarar ta tashi ne daga shagon wata mata da ke sayar kalanzir, daga nan ne kuma wutar ta kama sauran shaguna.

Ana fargabar cewa matar da ’ya’yanta na daga cikin wadanda karar kwana ta cimmasu sanadiyar gobarar.

Aminiya ta ruwaito cewa, kawo yanzu ba a san adadin mutanen da suka kone a gobarar ba a yayin da a lokacin daukar rahoton jami’an kwana-kwana ke ci gaba da kokarin kashe wutar.