Kimanin mutum 20 da dukiyoyi masu yawa ne suka salwanta a iftila’in gobara daban-daban da suka faru a watanni shidan farkon shekarar 2021 a Jihar Gombe.
Mataimakin Jami’in Ayyuka na Hukumar Kashe Gobara ta Jihar, Muhamood Salihu ne ya bayyana hakan a lokacin da yake zantawa da manema labarai a ofishin sa a Gombe.
Muhamood Salihu ya ce an kira jami’ansu kashe gobara har sau 172 a cikin wadannan watannin, inda mutane 607 suka sami raunuka, an kuma rasa dukiya ta biliyoyin Naira.
A cewarsa, gina karin hanyoyi da gwamnati ke yi a cikin garin Gombe ya kara saukaka musu aiki domin sun daina samun cinkoson ababen hawa a lokacin kai gudumawar gobara a wurare daban-daban na Gombe.
Shugaban hukumar ya kuma yi amfani da wannan damar inda ya shawarci jama’ar Jihar da cewa su kasance masu kula da abubuwan da ke amfani da wutar lartanki a wuraren aiki in an tashi don gudun faruwar gobara.