✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Gobara ta lakume kantin zamani a Moscow

Hukumar ba da agajin gaggawa a Moscow ta ce tana kyautata zaton rashin kiyaye matakan kariya ya haifar da gobarar.

A safiyar Juma’a aka samu aukuwar mummunar gobara a wani katafaren kantin zamani da ke Moscow, babban birnin kasar Rasha.

An ga jami’an kwana-kwana a yankin na kokarin kashe gobara don hana ta fadada zuwa wasu sassa.

Sai dai babu wani bayani daga hukumomin kasar kan ko an samu asarar rai da kuma adadin barnar da gobarar ta yi wa kantin.

Kwamitin bincike na kasar ya ce, ya soma bincike domin gano abin da ya haifar da gobarar.

Amma hukumar ba da agajin gaggawa a Moscow, ta ce tana kyautata zaton rashin kiyaye matakan kariya ne ya haifar da gobarar.