Hukumar Kashe Gobara ta Jihar Kwara ta ce, gobara ta lalata dukiya ta Naira biliyan 37.4 ranar Kirsimeti a Ilorin, babban birnin jihar.
Gobarar in ji hukumar, ta auku ne a wurare uku daban-daban a sassan babban.
- ’Yan bindiga sun sace mutum 100, sun sanya haraji a Neja
- NAJERIYA A YAU: Abin Da Ya Kamata Ku Sani Kan Ranar Kyauta A Addinin Kirista
Ta ce, duka gobarar sun auku ne a gidaje inda jama’a ke da zama a sassan Ilorin, babban birnin jihar, amma babu tabbacin samun asarar rai.
Cikin sanarwar da ta fitar ranar Litinin ta bakin jami’in yada labaranta, Hassan Adekunle, hukumar ta ce kokarin da jami’anta suka yi wajen kashe gobarar ya sa an kare dukiya ta Naira miliyan 765.6 daga lalacewa.
Ta kara da cewa, wuraren da aka samu aukuwar gobarar sun hada da yankin Balogun Fulani da gidan Okoosi da kuma gidan Abolarinwa, baki dayansu a cikin Ilorin.
Rahotanni sun ce, an danganta aukuwar duka gobarar da matsalar wutar lantarki.