Gobara ta tashi a kasuwar Karmo da ke Babban Birnin Tarayya Abuja, inda ta yi sanadin asarar kayayyakin makudan miliyoyi.
Kayayyakin sun kone ne a kasuwar yayin da wutar ta tashi da misalin karfe 12:20 ma daren Laraba.
- Mun gaji da gafara sa kan matsalar tsaro – Malaman Kaduna ga Buhari
- ’Yan bindiga sun fara tuntubar iyalan wadanda suka sace a harin Kaduna
Shugaban kasuwar, Murtala Ibrahim, ya tabbatar da faruwar lamarin, inda ya ce akalla shaguna 300 ne suka kone kurmus a kasuwar kafin hukumomin kashe gobara su yi nasarar kashe wutar da misalin karfe 2:00 na dare.
Ya ce wani shagon sayar da kayan lemuka ne ya yi sanadin tashin wutar wadda ta shafi shaguna da dama sannan ta cinye dukiyoyin mutane.
“Da yawan ’yan kasuwa da suka ji labarin wutar sun garzaya amma jami’an ’yan sanda da ’yan banga sun yi kokarin hana su shiga wutar saboda dimuwa.
“Wasu daga cikinsu sun yi kokarin fasa shagunansu don su dauki asusun da suke adana kudadensu, amma akwai hatsarin gaske a hakan,” cewar Ibrahim.
Idan ba a manta ba, a watan Oktoban bara, Aminiya ta rawaito yadda irin wannan gobarar ta tashi a kasuwar.
Sai dai wani dan kasuwa Shehu Ahmad ya ce wannan karon gobarar ta fi muni, inda aka yi harsashen sama da shaguna 300 sun kone.