Wata gobara da ta tashi a babbar kasuwar Onitsha da ke jihar Anambra da safiyar Litinin ta yi sanadiyyar konewar shaguna da dama.
Wata majiya ta tabbatar wa Aminiya cewa har zuwa lokacin hada wannan rahoton, kasuwar na ci ci gaba da ci da wutar.
- Qatar 2022: Zafin cin kwallon Moroko ya haddasa tarzoma a Belgium
- Yawan mutanen da suka mutu a girgizar kasar Indonesia sun kai 321
Wani dan kasuwar, Obi Barth Ifediora, ya tabbatar da cewa gobarar ta tashi ne a layin da ake kira da ‘Kano Street’ na kasuwar.
Bayanai dai sun nuna gobarar ta fara ne wajen misalin karfe 1:00 na daren Lahadi, kuma duk wani yunkurin kashe ta daga jami’an kashe gobara na jihar, ya ci tura.
Shugaban Hukumar Kashe Gobarar ta Jihar, Martin Agbili, wanda ya tabbatar da aukuwar gobarar ya ce da jin labarin suka aike da jami’ansu zuwa wajen.
“Ya zuwa yanzu, sun je sun cika motocin kashe gobara har sau biyu, yanzu kuma sun tafi su sake cika ta a karo na uku,” inji Martin.
Sai dai har zuwa lokacin hada wannan rahoton, ba a kai ga gano musabbabin tashin gobarar ba.