✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Gobara ta kone shaguna 19 a Kasuwar Rimi a Kano

Kakakin hukumar ya ce ba a samu asarar rai a gobarar ba.

Wata gobara da ta tashi da yammacin Laraba ta lakume shaguna 19 a Kasuwar Rimi da ke Jihar Kano.

Hukumar Kashe Gobara ta Jihar, ta tabbatar da faruwar lamarin ta wata sanarwa da kakakin hukumar, CSC Saminu Yusuf Abdullahi, ne ya bayyana haka yayin da yake zantawa da Aminiya.

Abdullahi, ya ce ma’aikatan sun samu kiran gaggawa da misalin karfe 01:46 na safiyar ranar Laraba daga wani Ahmad Tijjani cewa gobara ta tashi a kasuwar.

“Da samun labarin, sai muka yi gaggawar aike wasu jami’anmu da motar kashe gobara zuwa wurin da lamarin ya faru da misalin karfe 01:55 na safe domin kashe gobarar domin kada ta shafi wasu shaguna

“Lokacin da jami’anmu suka isa wurin sun tarad da ginannun shaguna 14 da rumfuna guda biyar duk sun kone kurmus, haka kuma wani masallachi da ke wurin shi ma ya kone.

“Jami’anmu sun yi kokari inda suka yi nasarar kashe wutar don gudun fantsamarta a wasu shaguna,” in ji shi.

Sai dai ya ce ba a samu asarar rai ba, kuma babu wanda ya jikkata a lamarin, kuma ana ci gaba da binciken musabbabin tashin gobarar.