Rumfuna 150 aka rawaito sun kone sakamakon gobara a babbar kasuwar garin Kachako da ke yankin Karamar Hukumar Takai a Jihar Kano.
Wannan na zuwa ne ’yan kwanaki bayan aukuwar makamanciyar wannan gobarar a kasuwar tumatir da ke Badume a Karamar Hukumar Bichi a jihar, inda sama da rumfuna 200 suka kone.
- An gano Kananan Hukumomi da ke biyan ma’aikatan bogi albashi a Anambra
- Ya kashe abokinsa da kahon dabba saboda ya ki saya masa giya
Mai magana da yawun Hukumar Kwashe Gobara ta Jihar Kano, Saminu Abdullahi, ya tabbatar cewa iftila’in ya faru ne ranar Litinin da rana.
“Da misalin karfe 01:13 na rana muka samu kira daga sashen kashe gobara na Karamar Hukumar inda muka isa wurin da misalin karfe 01:21 don kashe wutar,” inji shi.
Ya kara da cewa, kokarin da suka yi ya taimaka wajen kare kimanin rumfuna 800 daga konewa.
Ya ce ana zargin masu shaye-shaye ne tushen aukuwar gobarar.
Daga nan, jami’in ya gargadi al’ummar Kano da kewaye da su rika kula da yadda ake mu’amala da wuta, tare da tabbatar da suna kashe wuta kowcae iri kafin kwanciya barci.
Kazalika, ya ce ’yan kasuwa su rika tabbatar da kashe kayan wuta kafin barin shagunansu.