✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Gobara ta kone ofis 17 a Sakatariyar Gwale a Kano

Hukumar ta ce tana bincike domin gano musababbin tashin gobarar.

Hukumar Kashe Gobara ta Jihar Kano ta tabbatar da afkuwar gobara da safiyar ranar Laraba, wadda ta kone ofis 17 a sakatariyar Karamar Hukumar Gwale.

Kakakin hukumar, Alhaji Saminu Abdullahi ne, ya tabbatar wa da kamfanin dillancin labarai (NAN) a Kano.

Abdullahi, ya ce lamarin ya faru ne da sanyin safiyar Laraba.

“Mun samu kiran waya da misalin karfe 03:43 na safe daga Abdullahi Hassan cewa gobara ta tashi a sakatariyar Gwale.

“Bayan samun labarin, mun aike da motar kashe gobara zuwa wurin da abin ya faru domin kashe gobarar,” in ji shi.

Abdullahi ya ce benen da ke da ofis 17, ya lalace gaba daya, sannan kone sashen wasu motoci uku, ciki har da ta daukar marasa lafiya.

Ya ce hukumar na binciken musabbabin tashin gobarar.