Akalla kwamfutoci 100 ne suka salwanta sakamakon wata gobara da ta tashi a Sashen Nazarin Kwamfuta na Kwalejin Ilimi da ke Zariya a Jihar Kaduna.
Jami’an kashe gobara sun yi kokarin kashe wutar da ta tashi da misalin karfe 9 ja safiyar Asabar, lokacin da ma’aikatan kwalejin ba sa aiki.
- Gobara ta kashe mutum 49 a Bangladesh, ta jikkata kusan 300
- ISWAP ta kashe wani Babban Kwamandan Boko Haram a Borno
Shugaban Kwalejin, Dokta Suleiman Balarabe, ya ce wutar ta tashi ne sakamakon matsalar wutar lantarki, wanda hakan ya shafi kayan aikin sashen.
Ya kara da cewa, yana daga cikin tsarin Kwalejin na kashe kayan wutar lantarki a duk lokacin da aka tashi daga aiki, amma ya bada tabbacin za a musanya na’urorin da suka kone.
Har wa yau, ya ce sun dauki matakin kauce wa sake faruwar hakan a gaba.
Ya ce, “Zan sa a fito da wasu kwamfutoci da hukumar TETFund ta ba mu a baya don bai wa dalibai damar ci gaba da amfani na wucin gadi kafin lokacin da za a gyara ginin da ya kone.
“Dole zan gode wa kokarin da ABU Kongo da jami’an kashe gobara na Jihar Kaduna suka yi, wajen kawo mana dauki a kan lokaci.”