✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Gobara ta kone gidan Kwamishina a Ogun

Babu asarar rai da aka samu a gobarar

Gobara ta kone gidan Kwamishinan Harkokin Gona na Jihar Ogun a ranar Alhamis.

Iftila’in ya faru ne a yankin Kemta Idi-Aba da ke Abeokuta, babban birnin jihar.

Ya zuwa hada wannan labari ba a samu cikakken bayani ba kan dalilin aukuwar gobarar.

Kwamishinan, Dokta Odedina shi ne wanda ya tabbatar da aukuwar gobarar, inda ya ce babu wanda ya rasa ransa a musibar da ta auku.

Ya ce yana wajen aiki lokacin da aka kira aka sanar da shi abin da ya faru, wanda kafin isarsa makwabtansa sun taimaka wajen janye motocinsa daga gidan.

Daraktan Hukumar Kwana-kwana na Jihar Ogun, ya ce da alama wutar ta samo tushe ne daga dakin girke-girke na gidan.