✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Gobara ta kone ATM 6 na Bankin Zenith a Kano

Gobarar ta kone injinan ATM guda uku kurmus, wasu uku kuma sun dan ci wuta

Wata gobara da ta tashi da yammacin ranar Talatar nan ta kone injinan cirar kudi na ATM guda shida na Bankin Zenith da ke kan titin Tafawa Balewa a Karamar Hukumar Nasarawa da ke Jihar Kano.

Hukumar Kashe Gobara ta Jihar Kano ta ce gobarar ta cinye injinan ATM guda uku kurmus, wasu uku kuma suka ci wuta kadan.

Da yake tabbatar faruwar lamarin a wata sanarwa da jami’in hulda da jama’a na hukumar, Saminu Abdullahi, ya fitar ya ce hukumarsu ta samu kiran waya da misalin karfe 12:06 na rana daga wani Ghali Muhammad cewa gobara ta tashi a wuraren cirar kudin na injinan ATM.

“Daga samun wannan labarin, mun yi gaggawar tuna jami’anmu da motocin kashe gobara zuwa wurin da lamarin ya faru da misalin karfe 12:11 na rana, domin kashe gobarar domin kada ta shafi sauran na’urorin ATM din,” inji shi.

Abdullahi ya alakanta aukuwar lamarin da tartsatsin wutar lantarki daga injinan na ATM.

Wannan gobara ta tashi ne washegarin da aka wayi gari da wata a Kasuwar Kayan Abinci ta Singa da Kano, wadda ita ce ta hudu da aka samu gobara a kasuwannin Kano cikin mako biyu.