✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Gobara ta kashe mutum 90 a Kaduna a wata 9

An an samu gobara sau 436 daga watan Janairu zuwa Satumba a fadin Jihar Kaduna

Mutum 90 sun rasu, wasu 76 sun jikkata sakamakon gobara a Jihar Kaduna a cikin wata tara na farkon shekarar 2022 da muke ciki.

Hukumar Agajin Gaggawa ta Jihar Kaduna (KADSEMA) ta ce an samu gobara sau 436 daga watan Janairu zuwa Satumba a fadin jihar.

Da yake jawabi a taron wayar da kan jama’ar jihar kan gobara, Kodinetan Shiyyar Arewa maso Yamma na Hukumar Agajin Gaggawa ta Kasa (NEMA), Imam Garki, ya ce yawancin gobara da ake samu, dan Adam ne ke haddasawa.

Don haka ya yi kira gare su da su rika daukar matakan hana tashinta a kowane lokaci.

Ya ce wayar da kan al’umma a wannan lokaci na da muhimmanci ganin cewa hunturu, wanda shi ne lokacin aka fi samun gobara, ya kara matsawo.

“NEMA, a matsayin ja-gaba a kasa waje yaki da bala’o’i, tana wayar da kan gwamnatocin jihohi da hukumomi da daidaikun mutane kan matakan da suka fi dacewa su dauka,” in ji shi.

Taron wayar da kan wani bangare ne na taron kara wa juna sani na kwana uku da hadin gwiwar Hukumar Kashe Gobara ta Kasa da kuma Christian Aid/COOPI.