Akalla mutum 64 ne suka mutu bayan wata gobara ta tashi a wurin killace masu cutar COVID-19 a Kudancin kasar Iraki, kamar yadda gwamnatin kasar suka sanar a ranar Talata.
Kazalika, Sashen Lafiya na gundumar Dhi Qar ya tabbatar da jikkatar mutum 50 sanadiyyar gobarar.
- Buhari zai gana da duk Sanatoci 109 a daren Talata
- Hisbah ta kama mutum biyar da ake zargi da Luwadi a Kano
Gobarar dai ta tashi ne a ranar Litinin a asibitin Al-Hussein da ke birnin Nasiriyah a yankin Dhi Qar, mai tazarar kilomita 375 daga babban birnin kasar, Bagadaza.
Ma’aikatan asibitin sun tabbatar da gobarar ta ritsa da majinyata da kuma ma’aikatan asibitin sama 60.
Sun ce gobarar ta kone dakin jinyar marasa lafiyar da ka iya daukar majinyata 100.
Tuni dai Firaministan kasar, Mustafa Al-Kahdimi ya ba da umarnin gudanar a bincike tare da gano musababbin tashin wutar.
Ya zuwa yanzu babu wata sanarwa ko binciken da ya gano abin da ya haifar da gobarar.
Ko a watan Afrilu ma an sami irin wannan gobarar, da ta tashi a babban birnin kasar na Bagadaza wacce ta kashe sama da mutum 80.
Shugaban kasar, Barham Salih ya bayyana gobarar a matsayin wata ‘mummunar kaddara’. (NAN).