Akalla mutum 49 ne suka mutu, sama da 300 kuma suka jikkata bayan wata mummunar gobara ta tashi a wata ma’ajiyar kwantenoni da ke kasar Bangladesh.
Gobarar dai wacce ta tashi a tashar da ke garin Sitakunda mai nisan kilomita 40 daga birnin Chittagong, da daren Asabar, ta kuma yi sanadiyyar fashewar abubuwa da dama.
- Dokar hana acaba: Gwamnatin Legas ta ragargaza babura 2,000
- Gidan abinci ya hana masu hijabi da jallabiyya shiga cikinsa a Saudiyya
Babban likitan birnin Chittagong, Elias Chowdry ya shaida wa gidan talabijin na Aljazeera cewa adadin wadanda suka mutu yanzu ya kai 49.
Ya kuma ce fashewar abubuwan da ta ci gaba da aukuwa bayan gobarar ta kuma yi sandiyyar jikkatar mutum sama da 300.
“Akwai yiwuwar adadin mutanen da lamarin ya shafa ya karu a nan gaba, saboda wasu daga cikinsu na cikin mawuyacin hali,” kamar yadda Elias ya shaida wa Kamfanin Dillancin Labaran Faransa (AFP).
Daga cikin mutanen da suka mutu a gobarar dai har da wasu ma’aikatan kashe gobara su shida.
Bugu da kari, kimanin ’yan kwana-kwana 21 da ke kokarin kashe wutar ne suka sami munanan raunuka.
Gobarar da fashewar abubuwan sun kuma yi sanadin farfashewar gilasan tagogin gine-ginen da ke kusa da wajen da lamarin ya faru.
Rahotanni dai sun ce fashewar ta kuma yi tasiri sosai, inda ta rika girgiza gine-gine tun daga nisan kilomitoci da dama.
Har zuwa safiyar Lahadi dai ’yan kwana-kwana na ta kokarin kashe gobarar.