✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Gobara ta kashe mutum 41 suna tsaka da ibada a coci a Masar

Cocin dai na dauke da kusan masu ibada 5,000 lokacin da wutar ta tashi

Akalla mutum 41 ne suka mutu, wasu 14 kuma suka ji raunuka bayan wata gobara ta tashi a wata coci da ke birnin Giza da ke kusa da Cairo babban birnin kasar Masar.

Hukumar Lafiyar Kasar ce ta tabbatar da adadin, inda kuma ta ce tuni ta aike da motocin daukar marasa lafiya, kuma tuni an garzaya da kimanin mutum 55 asibitocin yankin.

Wata sanarwar ’yan sanda ta ce binciken farko-farko na nuni da cewa tangardar wutar lantarki ce ta haddasa gobarar ta ranar Lahadi.

Kazalika, wasu majiyoyi guda biyu sun shaida wa kamfanin dillancin labarai na Reuters cewa gobarar ta tashi ne a daidai lokacin da masu ibada sama da 5,000 suka taru a cocin, lamarin da ya haifar da turereniya.

Tuni dai aka girke injinan kashe gobara guda 15 a wajen don kashe wutar, su kuma motocin daukar marasa lafiya suna ci gaba da kwasar wadanda suka jikkata zuwa asibitoci.

Tuni dai Shugaban Kasar, Abdel Fattah el-Sisi, ya kira jagoran cocin, Tawadros II, don mika ta’aziyyarsa kan lamarin.

Bugu da kari, Babban Mai Shigar da Kara na kasar, Hamada el-Sawy, ya ce za a gudanar da zuzzurfan bincike don gano musabbabin tashin gobarar.

A ’yan shekarun nan dai kasar ta Masar ta sha fama da yawan tashin gobara.

Ko a watan Maris din 2021, akalla mutum 20 sun mutu a wata masana’anta da ke gabashin birnin Cairo sanadiyyar gobarar.