✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Gobara ta kashe ma’aurata da yara 2 a Kaduna

Lamarin ya faru ne bayan an kawo wutar lantarki.

Wasu ma’aurata da ’ya’yansu biyu sun rasa rayukansu a wata gobara da ta tashi a layin Dangan Waya da ke unguwar Rimaye a yankin Rigasa na Karamar Hukumar Igabi a Jihar Kaduna.

Lamarin ya faru ne da misalin karfe 11:00 na daren Lahadi yayin da ma’auratan da aka bayyana sunayensu da Musa da Zaliha tare da ’ya’yansu hudu suke tsaka da barci a daki.

Aminiya ta gano cewa ’ya’yansu biyu sun samu raunuka amma makwabta sun ceto su.

Wani makwabcin mutanen da lamarin ya ritsa da su, wanda ya bayyana kansa a matsayin Suleiman, ya ce gobarar ta tashi ne jim kadan bayan an kawo wutar lantarki.

“Bayan kawo wutar lantarki da misalin karfe 11:00 na dare, sai na ji wata kara mai karfi. Na yi tsammanin taransifomarmu ce ta yi wannan karar, amma daga bisani na ga hayaki na fitowa daga dakin makwabcinmu.

“Mun yi kokarin kashe gobarar amma ta riga ta mamaye dakin baki daya. An ceto yara biyu amma uban da matarsa ​​da wasu yara biyu sun mutu a gobarar,” inji shi.

Hakimin kauyen na Makera, Malam Isiyaku Abdulwahab Umar, ya tabbatar da faruwar lamarin, inda ya bayyana shi a matsayin annoba.

Ya yi addu’ar Allah ya jikan wadanda lamarin ya shafa tare da yi wa yaran biyu da suka jikkata fatan samun sauki.

Tuni dai aka yi jana’izar wadanda suka mutu kamar yadda addinin Musulunci ya tanada.