✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Gobara ta kashe dan shekara 3 da mahaifiyarsa a Kano

Gobarar ta kone gidan kurmus.

Mazauna titin Bala Barodo da ke unguwar Gandun Albasa a Jihar Kano sun wayi gari cikin juyayi bayan da wata gobara da ta tashi da tsakar dare ta kashe wata uwa mai shekaru 35 tare da danta mai shekaru uku sun tsaka da barci.

Wani likita da ke bakin aiki a Asibiti Kwararru na Murtala Muhammad da ke Kanon ya tabbatar da mutuwarsu.

Hukumar Kashe Gobara ta Jihar Kano ta tabbatar da faruwar lamarin ta bakin jami’in hulda da jama’arta, Saminu Yusif Abdullahi.

Abdullahi ya bayyana cewa lamarin ya auku ne a daren ranar Alhamis.

“Mun samu kiran neman agajin gaggawa da misalin karfe 2:07 na dare daga wani Ibrahim Ashiru kuma nan take muka aika da tawagarmu zuwa wurin da abin ya faru da misalin karfe 2:11 na wannan dare.

“Ma’aikatanmu sun riski gidan mai tsayi da fadin kafa 75 ya kone kurmus a sakamakon gobarar.

Abdullahi ya ce duk da cewa an ceto wadanda abin ya shafa a sume kuma aka mika su ga wani jami’in yan sanda, Insifeta Shehu Lawan na ofishin ‘yan sanda da ke unguwar Kwalli, inda ya garzaya da su Asibitin Kwararru na Murtala Muhammad kuma likitocin da ke bakin aiki suka tabbatar da mutuwarsu.