Wata ma’ajiyar tankokin mai mallakin kamfanin mai na Oando a unguwar Ijora, jihar Legas ta kama da wuta.
Ya zuwa yanzu dai ba a kai ga gano musabbabin gobarar da ta tashi da safiyar Alhamis ba, amma ma’aikatan kwana-kwana na ci gaba da kokarin ceto mutanen da ke cikin wurin.
Jami’in Shiyya na Hukumar Agaji ta Kasa (NEMA) a Jihar, Ibrahim Farinloye ya tabbatar da aukuwar lamarin, ko da yake ya ce hukumarsa na yin bakin kokarinta wajen ganin ta ceto dukkannin mutanen da ke cikin ginin.
Ya ce tuni ’yan kwana-kwana daga Hukumar Kula da Jiragen Ruwa ta Najeriya, (NPA), Hukumar Kashe Gobara ta Kasa da kuma Hukumar Kula da Lafiyar Teku ta Najeriya (NIMASA) suka far aiki haikan domin kashe gobarar.