✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Gobara ta hallaka uwa da ‘ya’yanta a Bauchi

Wata uwa tare da ‘ya’yanta biyu sun rasu a wata gobara a kauyen Riban Garmu da ke Karamar Hukumar a Jihar Bauchi. Wani ganau, Ibrahim…

Wata uwa tare da ‘ya’yanta biyu sun rasu a wata gobara a kauyen Riban Garmu da ke Karamar Hukumar a Jihar Bauchi.

Wani ganau, Ibrahim Kirfi ya shaida wa Aminiya cewa duk kokarin da aka yi na ceto matar da ‘ya’yanta ya gagara.

Ya ce wasu mutum hudu kuma sun samu raunuka kuma an garzaya da su zuwa asibiti domin samun kulawa.

Ibrahim ya ce Ya ce gobarar ta kone gidan mai dakuna hudu a yayin da mamatan suke barci.

Ya ce ana zargin tartsatsin wutar lantarki ne ya haddasa tashin gobarar a cikin tsakar dare.

Dan Majalisar Dokokin Jihar Bauchi Mai Wakiltar Mazabar Kirfi, Abdulkadir Umar Dewu, ya kai wa iyalan ziyarar ta’aziyya da dubiya a madadin Gwamna Bala Mohammed.

Ya yi addu’ar Allah Ya jikan su, sannan ya bukaci iyalan da su dauki abin da ya faru a matsayin kaddara.

Dan Majalisar ya kuma ba wa iyalan tallafi na N250,000.

Wani daga cikin shugabannin al’umma a yankin, Malam Muhammadu Riban Garmu ya bayyana godiyarsu ga gwamnan jihar da kuma dan majalisar.