Asafiyar Talatar da ta gabata ce akalla mutum 17 suka rasu a wata gobara da ta faru a wani otel da ke Unguwar Karol Bagh a birnin Delhi da ke kasar Indiya.
Wadanda suka gane wa idanunsu aukuwar lamarin sun ce a cikin wadanda suka rasu a gobarar akwai wata mata da danta, wadanda suka yi kokarin kubuta ta tagar ginin.
Hukumomi a kasar sun cewa sun ceto mutum 35 daga cikin ginin, wadansu daga cikinsu sun samu raunuka wadansu kuma an garzaya da su asibiti.
Sashin Hausa na Rediyon BBC ya ruwaito cewa, wadansu daga cikin wadanda suka ga lamarin kuma wadanda suka nadi bidiyo a wayoyinsu, sun nuna yadda mutane ke tsalle daga ginin otel din domin su tsira daga wutar.
Daya daga cikin jami’an kashe gobara da suka yi aikin kashe wutar mai suna Bipin Kenta, ya ce yanzu haka sun fara gudanar da bincike a kan musabbabin tashin gobarar.
A bangaren, Firayi Ministan Indiya, Narendra Modi ya bayyana jimaminsa a kan lamarin. Ya nuna alhininsa a turakarsa ta kafar sadarwar zamani ta Twitter.