✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Gobara ta halaka mutum 3, ta kone shaguna 100 a kasuwar Badume da ke Kano

Daga cikin mutanen da suka rasu, biyu maza ne, daya kuma mace ce

Wata gobara da ta tashi a kasuwar sayar da kayan miya ta Badume da ke Karamar Hukumar Bichi a Jihar Kano ta yi sanadin rasuwar mutum uku ta kuma kone shaguna kusan 100.

Aminiya ta gano cewa gobarar ta fara ne daga wani shago da ke tsakiyar kasuwar.

A cewar Kakakin Hukumar Kashe Gobara ta Jihar Kano, Saminu Yusuf Abdullahi, sun sami kiran gaggawa daga wani mai suna Malam Tsalha daga kasuwar.

Nan take a cewar Kakakin jami’ansu suka bazama zuwa wajen, inda suka iske mutum uku, mace daya da maza biyu, ciki har da wani tsoho wutar ta ritsa su a ciki.

Saminu ya ce daga bisani sun sami nasarar ceto mutanen uku wadanda ke cikin mawuyacin hali, amma daga bisani likita ya tabbatar da rasuwarsu.

Ya kuma ce akalla shaguna 100, galibinsu na wucin-gadi ne suka kone kurmus, kafin su sami nasarar kashe wutar don dakile ci gaba da yaduwarta.

Kakakin ya ce har yanzu suna ci gaba da bincike domin gano musabbabin gobarar.

Daga nan sai ya yi kira ga jama’a da su rika yin taka-tsan-tsan wajen yin amfani da kayan lantarki don gujewa aukuwar gobarar.