✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Gobara ta babbake unguwar marasa galihu a Saliyo

Iftila’in na cikin dare ya shafi dubban mutane a unguwar talakawan.

Wata unguwar marasa galihu ta kone sakamakon wata gobara a yammacin Laraba a Freetown babban birnin kasar Saliyo.

Mahukuntan birnin sun ce iftila’in na cikin dare ya shafi dubban mutane, kodayake , du ba a gama tantance adadin mutanen ba.

“Wuta ta kone unguwar Susan’s Bay amma ba a san iya asarar barnar da aka yi ba amma akwai yiwuwar dubunnan lamarin ya shafa.

“Za mu yi karin bayani nan gaba. Ku ci gaba da mutanen da abin ya shafa cikin addu’o’inku!,” inji Majalissar Birnin Freetown a cikin wani sako da ta wallafa a cikin daren.

Yawancin gidajen da ke unguwar marasa galihu da ke Susan’s Bay marasa nauyi ne da aka yi da kwano da wasu kayan gwangwan.

Jakadan Tarayyar Turai a Saliyo, Tom Vens, ya ce EU na duba hanyoyin aika kayan taimako ga wadanda lamarin ya shafa.

“Za mu yi tunani tare da (hukumomi) kan matakan da ake bukata don rage barazanar irin wannan masifar sake faruwa,” inji shi a shafin Twitter.

Kasar Saliyo mai arzikin lu’u-lu’u daya ce daga cikin kasashen da talauci ya fi yi wa katutu a duniya.

Tattalin arzikinta ya lalace sakamakon yakin basasa na 1991 zuwa 2002 wanda ya lakume rayukan mutane 120,000.

Sannan kuma cutar ta Ebola wacce ta fara daga 2014 zuwa 2016 ta kara durkuwar da tattalin arzikin kasar.

Bugu da kari, ga tashin gwauron zabon farashin kayayyaki a kasuwannin  duniya sakamakon annobar cutar coronavirus.