Wata gobara da ta tashi cikin ta lalata wani ɓangare na Asibitin Ago da ke kan titin Ago Palace, Okota, a Jihar Legas.
Gobarar ta fara ne da misalin ƙarfe 8:30 na daren ranar Juma’a, inda ta shafi wani sashe na ginin mai bene hawa ɗaya, inda asibitin yake.
- Gobara ta hallaka mutum 2 a sansanin ’yan gudun hijira a Borno
- Ramadan: Saudiyya ta bai wa Kano da wasu jihohi kyautar dabino katan 1,250
Likitoci da marasa lafiya da ke cikin asibitin sun tsere domin tsira da rayukansu yayin da wutar ta bazu.
Babban Sakataren Hukumar Bayar da Agajin Gaggawa ta Jihar Lagos (LASEMA), Dokta Olufemi Damilola Oke-Osanyintolu, ya ce jami’ansu sun isa wajen gobarar da misalin ƙarfe 8:45 na dare.
Binciken da LASEMA ta gudanar ya nuna cewa gobarar ta faru ne sakamakon matsalar wutar lantarki.
Rahotanni sun nuna cewar babu wanda ya rasa ransa ko ya jikkata.
Jami’an kashe gobara daga LASEMA da LRU da sauran masu bayar da agajin gaggawa sun haɗa kai don shawo kan gobarar tare da hana ta bazuwa zuwa wasu gine-gine da ke kusa da asibitin.