✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Gobara daga kogi: Marubuta ina mafita?

Rubutu wani abu ne na baiwa wanda ba kowa ke samun damar yi ba, sai wadansu kebabbun mutane da Allah Ya saukaka musu. Rubutu ya…

Rubutu wani abu ne na baiwa wanda ba kowa ke samun damar yi ba, sai wadansu kebabbun mutane da Allah Ya saukaka musu. Rubutu ya tattara duk nau’ukan abubuwan da za a rubuta bisa takarda da nufin isar da sako, walau ta hanyar waka ko labarin kirkira ko kuma rubutaccen wasan kwaikwayo.
A yayin rubutu, marubuci kan yi amfani da hikima da salo da sarrafa harshe da azanci da jeranta tunani da jigo da sauran dabaru, ta haka ne zai cusa sako ko tunanin da yake son sa wa makarancin rubutun nasa a zuciya.
A kasashen da suka ci gaba, ana girmama marubuta kwarai, ana daukarsu  muhimman mutane masu daraja da wata baiwa kebabbiya, don haka akan killace su. Muhimmancinsu ya fi na ’yan siyasa ko gungun mutane da amfaninsu na wani takaitaccen lokaci ne, sabanin marubuci da a kowane zamani, a kowane lokaci, a kowane yanayi yana ba da gudummawa ga mutane; hatta a lokutan yaki. Don haka a wadancan kasashe, manyan kamfanoni na daukar nauyin buga aikin marubuci don yada shi a cikin al’umma. Hakan ya sa marubutan waje ba su samun wahalar dab’i, tacewa, ingancin aiki da sauransu. Hatta a nan kasar, a shekarun baya (kafin 1960) Turawan mulkin mallaka sun tallafi wadansu marubuta da suka san suna da baiwar rubutu, har ta kai an samar da hadadden littafin ‘Magana Jari Ce’ daga na daya zuwa na uku. Haka nan aka ci gaba da tafiya ana sanya gasa tsakanin marubuta, wadda ta zama allurar da ta samar da litattafai masu matukar alfanu (ba sai na ambaci sunayensu ba); wadanda har yanzu ana amfani da su a manhajar karatu a makarantunmu na zamani.
A shekarun 1980 zuwa 1990 ne (bayan an samu ’yancin kai daga hannun Turawa) aka ci gaba da rubuta littattafai, sai dai a wancan karon takun ya sauya salo, domin an samu marubuta da suka yi ta rubuce-rubuce a kan rayuwar matasa, abin da har yanzu ake samun kwararowar sababbin marubuta maza da mata.
Abin da ya sa na ce takun ya sauya salo kuwa shi ne, a wadancan shekarun sai ya zama marubuci ne zai rubuta littafinsa da kansa ya buga ko ’yan kasuwa su saya su buga ko kwafe nawa ne sai a kai kasuwa. A lokacin, littattafan Hausa na matukar samun tagomashi, musamman a tsakanin matasa, duk da cewa wadansu mutane a wancan lokacin na cewa marubutan na bata tarbiyyar yara, suna koya musu kin karatu (na makaranta) amma duk da haka marubutan sun daure sun ci gaba da rubutunsu, kuma sakonsu ya taba al’umma sosai ta yadda suka ci nasarar yaki da auren dole a kasar Hausa (tunda mafi yawan litattafan a kan soyayya aka gina jigoginsu).
dan uwa, ba ina wannan rubutu ba ne don in ba ka tarihin rubutun littafi a kasar Hausa, a’a, ina yi ne don in nuna maka yadda marubuci yake da daraja da kimar da a yanzu wadansu marubuta sun barar da ita; suna gina matsalar da daga baya su za su yi kuka da ita.
Daga cikin abin da ya tallafa wa marubuta a wancan lokaci (wajen isar da sakonninsu) akwai karanta littafin a gidajen rediyo, yin hakan kuwa ya sa hatta mutanen da ba su karatu sukan saurari littafi a rediyo kuma su amfana da baiwar marubucin. Kuma aka yi sa’a duk da sukar da ake yi wa marubutan, an samu mutanen da suka yi musu kyakkyawar fahimta suka san muhimmancin aikinsu. Ta yadda ba a karanta littafin mutum har sai an sanar da shi (kila idan ya ce ba ya so ba za a karanta ba), sannan gidan rediyon da kansa ko makarancin, ba su ne ke zabar littafi da kansu ba, a’a, masu karatu ne kan aiko da littafin a ambulan hade da wasika ta neman alfarmar a karanta littafin. Duk da haka ba a karantawa sai an yi nazarin littafin an tabbatar babu matsala, kuma a karshen shirin, makarancin littafin yakan fadi sunan wanda ya aiko da littafin (don a karanta) tare da sunan marubucin da sunan littafin. Na saurari littattafai da yawa a wancan lokacin.
Sai dai a yanzu abin ya sauya salo, ta yadda marubuci ne da kansa zai nemi a karanta littafinsa a gidajen rediyo, saboda marubutan sun yi wata irin fahimta cewa sai ana karanta littafin mutum sannan zai samu ciniki a kasuwa. Yin haka kuwa babban kuskure ne, domin yana zubar da kimar marubuci a idanun gidan rediyo ko mai karantawar. A hankali sai wadansu su fara ganin ai alfarma ake yi wa marubucin, ana taimaka masa. Wani abin takaici shi ne, yadda daga zarar an kammala karanta littafi, to fa shi ke nan an daina yayinsa, kada marubucin ya sa ran za a kuma sayen littafinsa ko da kwafi daya ne a kasuwa, wato littattafanmu sun fara tashin gishirin andurus, in dai an fara karanta su a rediyo.
In kuwa haka ne (kuma haka din ne), to sai dai mu ce ga gobara daga kogi nan, maganinta sai dai Allah.
Ana so littafi ya zama na kowane zamani ba wai na makonni ko watanni ba. Akwai littattafan da har yanzu nemansu ake yi a kasuwa saboda sun rubutu, kuma ba a taba karanta wasunsu a gidajen rediyo ba, amma sun yi karko irin na dabino. Kada na kai ka da nisa dan uwa, duba wasu litatttafan da aka yi a shekarun 1990. Kwanan nan na ji wani babban marubuci sananne yana kokarin sauke littattafansa a yanar gizo sannan ya sake buga wasu.

Lawan PRP, ya aiko da wannan tsokaci ne daga Kano