Hukumar Kashe Gobara ta Jihar Kano ta ce mutum 166 ne suka rasu, sannan kuma an yi asarar dukiya ta Naira miliyan 358 da ta kone a shekarar 2022 da muka yi bankwana da ita.
Kakakin hukumar, Saminu Yusuf Abdullahi ne ya bayyana hakan cikin wata sanarwa da ya fitar a ranar Litinin.
- Brentford ta casa Liverpool a Firimiyar Ingila
- Bakin ciki ya sa Obasanjo ke sukar shugabanni — Garba Shehu
Ya bayyana cewa mutum 1,035 da dukiyar da ta kai kwatankwacin Naira miliyan 905 suka ceto a shekarar.
“Mun samu kiraye-kirayen gaggawa 736, da kuma wasu na jabu 208 a 2022.
“Mun kai dauki wurare 575 da aka samu hatsari a jihar, sai kuma dabbobi 6 da su ma muka ceto su a shekarar.
Abdullahi ya kuma ce da dama daga gobarar da aka samu a shekarar sanadiyyar iskar gas ce, da kuma amfani da kayayyakin lantarki marasa inganci.
Ya shawarci al’umma a wannan lokaci na sanyi, da su tabbatar sun kashe wutar jin dumi da wadataccen ruwa, gudun tashin gobarar.