Hukumar Kashe Gobara ta Jihar Kano, ta sanar da ceto rayukan mutum shida da dukiyar Naira miliyan 107 daga gobara 74 da suka faru a watan Fabrairun 2024, a jihar.
Kakakin hukumar, Alhaji Saminu Abdullahi ne, ya bayyana hakan a wata hira da Kamfanin Dillancin Labaran Najeriya (NAN), a ranar Juma’a a Kano.
- Za A Bi Kadun Kisan Sheikh Abubakar Mada — Gwamna Dare
- Anthony Joshua ya doke Francis Ngannou a damben ƙwararru a Saudiyya
Abdullahi, ya kuma ce mutum hudu ne suka rasa rayukansu, yayin da gobarar ta kone dukiyar Naira miliyan 64.
“Mun samu kiran kai agaji bakwai daga kiran waya 10 daga mazauna jihar,” in ji shi.
Ya shawarci jama’a da suke kula sosai da abin da ya shafi wuta da lantarki.
Kazalika, ya ce wasu daga cikin gobarar sun tashi ne sanadin gas din girki.
Har wa yau, ya ce akwai bukatar mutanen jihar suke neman bayanai game da abin da ya shafi gobara da hanyoyin kare ta.