✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

‘GOAT’: Ko nasarar Argentina za ta kawo karshen tababa tsakanin masoyan Messi da Cristiano?

Shin nasarar Argentina na nufin tababa tsakanin Messi da Cristiano kan GOAT ta zo karshe?

Daga karshe dai a ranar Lahadi, babban burin dan wasan kasar Argentina, Lionel Messi, na lashe wa kasarsa Kofin Duniya, ya cika.

Nasarar ta zo ne bayan Argentina ta doke Faransa ta hanyar bugun fanareti a wasan karshe na Gasar Cin Kofin Duniya ta 2022, wacce aka kammala a kasar Qatar.

Hakan dai ya sa Argentina ta kafa tarihin daukar kofin har sau uku, tun da aka fara buga shi a 1930.

Masana da masu sharhi kan harkokin wasanni sun yi amannar cewa an jima ba a yi gasar Cin Kofin Duniyar da ta kayatar irin wacce aka yi ta bana a Qatar ba.

To sai dai baya ga kayatattun wasanni 64 da aka fafata tun da aka fara gasar a ranar 20 ga watan Nuwamban da ya gabata, zuwa na karshe a ranar Lahadi, fitattun ’yan wasa ne suka kece wa kasashensu raini.

Bugu da kari, gasar ta dada zafafa muhawarar nan da magoya bayan ’yan wasannan biyu da suka fi kowa lashe kambun Ballon d’Or, wato Lionel Messi da Cristiano Ronaldo, kan wane ne asalin Sarki a duniyar kwallon kafa, wato GOAT, a takaice.

Kowane daga cikin magoya bayan na ganin gwaninsa ne Sarki, inda Cristiano ya buga wa Portugal, Messi kuma Argentina.

Amma sakamakon rashin nasarar da Portugal din Cristiano ta yi a hannun Maroko a wasan dab da na karshe, magoya bayan Messi sun samu abin fade, inda suke cewa gwaninsu ne Sarki, alabasshi idan kasarsa ta samu daga kofin.

Messi dai ya ce dama kofin shi kadai ya tsone masa ido da bai taba daga wa tawagarsa ba, kuma yanzu ke nan ana iya cewa burinsa ya gama cika a duniyar kwallon.

Sai dai abin jira a gani shi ne ko wannan muhawarar da tababa tsakanin Messi da Cristiano za ta kawo karshe da nasarar ta Argentina?