Tarihin rayuwa:
An haife ni a shekarar 1956 a Unguwar Tudun wada da ke karamar Hukumar Nassarawa cikin Jihar Kano. Na yi karatun firamare a makarantar T/wada Central a shekarar 1963. Sannan na tafi Kwalejin ’Yan mata ta Shekara a shekarar 1968 zuwa 1969. Daga nan sai na tafi makarantar sakandare ta WTC Kano daga shekarar 1970 zuwa 1974. Daga nan na samu aikin koyarwa inda na koyar a firamarens T/wada da ta Rimi da kuma ta Magwan. Daga nan sai na koma makaranta inda na samu takardar shaidar Malanta (NCE) a shekarar 1976 zuwa 1979. Bayan na gama karatun NCE sai na kama aiki da Ma’aikatar Ilimi ta Jihar Kano inda aka kai ni Kwalejin Commercial da ke kan titin Airport a matsayin malama. Ina wannan makaranta ne sai na koma karatu a Jami’ar Bayero inda na samu shaidar digiri a bangaren kimiyyar siyasa. Bayan na kammala sai na ci gaba da aikina na koyarwa har aka ba ni mukamin shugabar makaranta (Principal) mukamin da na rike tsawon shekaru 18. Na zauna a makarantu da dama wasu daga ciki sun hada da Kwalejin ’yan mata ta babura da ta Taura da ta danbatta da ta Sumaila da ta Shekara sai kuma a karshe na dawo makarantar da na yi karatu wato WTC, daga nan sai aka mayar da ni bangaren duba makarantu. Ina nan sai aka sake canza ni zuwa ofishin shiyya na Nasarawa a matsyain Darakta mai kula da shiyyar. Sannan daga baya aka mayar da ni shiyyar Dala. Daga nan sai aka ba ni Kantoma a karamar Hukumar Rimin Gado. Bayan mun gama sai aka mayar da ni sashen da ke bibiyar ayyukan makarantu kafin daga bisani aka sake mayar da ni sashen duba makarantu. Ina nan sai aka mayar da ni ma’aikatar da ke kula da makarantu masu zaman kansu da na al’umma da ke Jihar Kano.
Kafin na yi ritaya sai aka kai ni dakin karatu (Library) a matsayin Shugabar wurin, inda na zauna tsawon shekaru biyu. Daga nan ne kuma Gwaman Kano Dokta Abdullahi Umar Ganduje ya ba ni wannan kujera ta shugabancin Hukumar Ilmin Manya ta jihar.
Ayyukanta a Hukumar Ilimin Manya:
Kamar yadda sunan wannan hukuma ya nuna, muna kula da duk abin da ya shafi iliimin manya. A Jihar Kano muna da cibiyoyi da muke koyar da manya mata guda 48 baya ga na maza yayin da wasu ke daukar karatu da daddare wasu kuma da safe. Baya ga karatu da rubutu a waje daya kuma matan ana koya musu sana’o’i don dogaro da kansu. A yanzu haka mai girma Gwamna ya bayar da wasu kayayyakin aiki da za mu raba a wadannan cibiyoyi namu.
Hukumarmu tana da shiri na ilimintar da jama’a wanda ake da burin kowa ya samu ilimi. A kwanan nan ma gwamnatin Tarayya karkashin Hukumar da ke Kula da Ilimin Manya ta kasa ta kaddamar da shirin gangamin bayar da ilimi ga al’umma a Jihar Kebbi. A yanzu haka mu ma a matakin jiha muna shirye-shiryen yadda za mu gudanar da wannan shiri don ganin kowa ya ilimantu.
Gwamnatin Jihar Kano tana ba mu goyon baya dari bisa dari wajen gudanar da ayyukanmu domin a watan Fabrairun bana gwamnatin Jihar Kano ta kaddamar da wani shiri na koyar da jami’an sintiri wanda aka fi sani da bijilanti 3700. A yanzu haka ma sun gama rubuta jarrabawa na mataki na farko da suka yi. A lokacin da suke rubuta jarrabawar ma sai da Shugaban Hukumar Ilimin Manya ta kasa Farfesa Abba Haladu ya zo tare da ’yan tawagarsa don gane wa idanunsu yadda shirin yake gudana inda muka zaga kananan hukumomin Tofa da Dawakin Tofa da Gwale da sauransu. A yanzu ’yan bijilanti sun iya karatu da rubutu, haka kuma sun iya amfani da wayar hannu tare da rubuta gajeren sako, wanda a da sai dai su nemi taimakon wasu mutanen idan suna son yin amfani da wayar hannu. Nan ba da dadewa ba za su shiga mataki na biyu na karatu don bunkasa iliminsu. Alhamdulillahi kwalliya ta biya kudin sabulu. A yanzu haka ma shirye-shirye sun yi nisa inda za mu fto da tsari na koyar da jama’a Turanci ta hanyar rediyo wanda za mu rika gabatarwa a Gidan Rediyon Jihar Kano.
Nasarorin da ta samu:
Zan iya cewa babu babbar nasara musamman ga malamin makaranta irin yadda zai waiwaya baya ya ga irin daliban da ya koyar sun ilimantu sun kuma shiryu sun zama manyan mutane a cikin al’umma har sun kai ga fara bayar da tasu guddumawar ga al’umma. A yanzu haka dalibai da yawa da suka yi karatu a makarantun da na rike sun zama manyan mutane, wasu sun zama likitoci da malaman makaranta da injiniyoyi, wasu a gida Najeriya wasu kuma a kasashen wajen. Babu shakka hakan ba karamin abin alfahari ba ne ga malamin makaranta. Duk da cewa ana shan wahala kafin daliban su zama abin da ake so su zama amma Alhamdulillahi, duk da haka da muka daure muka rike harkar kula da yaran ga shi yanzu ya zama tarihi.
kalubalen da ta fuskanta:
Babu shakka aiki na cike da kalubale. Sai dai babban kalubalen da na fuskanta shi ne lokacin da aka rika kai ni kauyuka inda na fuskanci matsalar rashin wuta da ruwa. Mutum ya riga ya saba da rayuwar birni amma sai ga shi an kai mu kauye wanda kowa ya san rayuwar ba iri daya ba ce. Gaskiya wannan ba karamin kalubale ba ne, amma cikin taimakon Allah haka muka zauna muka gudanar da ayyukanmu cikin nasara.
Shi ma batun hada karatu da aiki da kula da gida shi ma kalubale ne, amma kasancewar akwai goyon baya na maigida da ’yan uwa da kuma uwa uba kudurin da mutum yake da shi cewa zai yi abin, sai ga shi mun yi nasara. A lokacin idan za ni makaranta nakan ajiye yara a wurin ’yan uwa ko mai aiki a cikin gida. A wannan lokaci maigida ya taka rawa sosai wajen bayar da gudummawa, domin ba don goyon bayansa ba da abubuwan ba za a samu cin galabansu ba.
Iyalinta:
Ina da ’ya’ya hudu da kuma jikoki goma. Ban da ’ya’yan ’yan uwa da na rike masu yawan gaske. Duka yaran sun yi karatu don a yanzu haka daya daga ciki ya dauko layin namu na koyarwa. Yana nan yana koyarwa a Jami’ar Bayero (BUK) a bangaren ilimi har ma ya zama Dokta (Phd).
Burinta:
Ni a yanzu ba ni da babban buri illa na cika da imani. Sai kuma ina burin na ga sauran yara masu tasowa sun zauna lafiya tare da taimakon junansu.
Abin da take so a tuna ta da shi:
Babu abin da yake burge ni a rayuwata irin taimakekeniya, watau ka taimaka wa dan adam kowane ne idan ya zo hanyarka ka taiamka masa da abin da za ka iya. Shi ma kuma ya yi kokarin taimaka wa wani a nan gaba, wannan shi zai sa a samu al’umma mai ci gaba. Ina ganin idan ba ka taimaka wa mutane sun samu hanyar cin abinci ba ina ganin kamar ba ka yi komai a rayuwa ba. Ina son idan an tashi tunawa da ni a tuna da ni a matsayin wacce ta bayar da gudummawa wajen taimakon al’umma, musamman harkar ilimin mata.
Mutane abin koyi:
Ba ni da wani abin koyi kamar Manzon (Allah SAW) da iyalinsa. Idan kin dauki Sayyidah Khdijah (Allah ya kara mata yarda) game da irin guddumawar da ta ba Manzon Allah (SAW) a lokacin da ya zo mata da batun addinin Musulunci. Abin da ta yi shi ne abin da ya kamata kowace mace ta yi wa mijinta yayin da ya zo mata da wani abu. Ta goya masa baya da kanta da duk abin da ta mallaka. A koyaushe ina ganin Manzon Allah da Ahlin gidansa a matsayin abin kwaikwaiyo.
Shawarata ga mata:
Shawarata ga mata tana da yawa, babbar shawarata ita ce ya kamata kowacce mace ta dauki hakuri da juriya musamman sha’anin abin da ya shafi tarbiyyar ’ya’yanta. Mata su daure kan al’amuran da ke faruwa a gidajen aure. Mu sani cewa ginshikin gida karfinsa yana ga mace idan aka samu jaruma zakakura wacce ta daure ta yi hakuri ta jajirce ta zauna a dakinta da dadi da rashinsa, ta kuma yi kokarin shawo kan dukkanin matsalolin da suke tasowa a gidanta, babu shakka za ta yi nasara. Haka kuma ’ya’yanta za su yi albarka. Za su zama masu tarbiyya zakakurai jarumai. Za kuma su fahimci rayuwa. Wani abin sha’awa kuma shi ne daga karshe idan ta tsufa ’ya’yan nan nata su za su kawo mata dauki. Ina kara maimaitawa cewa mata mu kula da ’ya’yanmu da tarbiyyarsu da kuma karatunsu. Sannan ina kara kira ga mata da mu zama masu biyayya ga mazajenmu, domin wannan ce kadai hanyar da za ta fisshe mu.
Ina kira ga mata da su nemi ilimi kasancewar su ne suke tarbiyyar ’ya’yansu, kasancewar zamansu a gida ya fi na iyaye maza, don haka akwai bukatar a ilimintar da mata. Idan an ilimatar da mace daya kamar an ilimantar da al’umma ne. kuma girma ba ya hana ilimi, don haka koda mace ta mnayanta za ta iya samun ilimi a cibiyoyin ilimin manya da ke fadin kasar nan.