✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Girgizar kasar Maroko: Cristiano Ronaldo ya bayar da tallafin otal dinsa

Ya bayar da otal din nasa ne mai daki 174 domin tsugunar da mutanen

Fitaccen dan wasan ƙwallon ƙafar nan, Cristiano Ronaldo ya bayar da gudunmawar otal dinsa mai suna Pestana CR-7 domin tsugunar da mutanen da girgizar kasar Maroko ta shafa.

Jaridar Marca ta kasar Spain ta raiwaito cewa ya bayar da gudunmawar ce ga otal din da yake birnin da da aka yi girgizar na Marakkech, a ranar Juma’a.

Girgizar kasar mai karfin 6.8 wacce ta fada wa birnin da ke kasar ta Arewacin Afirka, ta yi ajalin sama da mutum 2,000, wasu da dama kuma sun jikkata.

Ana haka ne dai ƙungiyoyi da dama a birnin suka bayar da tallafi ga wadanda lamarin ya shafa.

Cristiano dai ya bi sahu inda ya bayar da otal din nasa na alfarma mai dakuna 174.

Otal din dai na da wajen ninkaya da na motsa jiki da wajen cin abinci da kuma filin wasa.