Aƙalla mutum tara ne suka mutu bayan wata girgizar kasa mai karfin maki 7.4 da ta auku a gabar tekun gabashin Taiwan da safiyar ranar Laraba.
Fiye da mutane 700 ne suka samu raunuka yayin da ake ci gaba da aikin ceto bayan afkuwar girgizar kasar.
- Taurarin Zamani: Sadiq Muhammad Yelwa (Ɗan Gwamna)
- Tinubu ya rattaba hannu kan dokar bai wa ɗalibai rancen kuɗin karatu
Girgizar ƙasar ita ce mafi girma da ta afku a tsibirin a cikin shekaru 25.
Kimanin mutane 2,400 ne suka mutu a shekarar 1999 lokacin da wata girgizar kasa mai ƙarfin maki 7.7 ta afku a Taiwan a tsakiyar dare.
Shugaba Tsai Ing-wen ta ba da umarnin a jibge sojoji a faɗin yankunan da lamarin ya shafa.
“Rundunar sojin kasa za ta biya bukatun kananan hukumomi tare da ba da tallafi don tabbatar da tsaron rayuka da dukiyoyin ‘yan kasa,” in ji Tsai a wata sanarwa da ta fitar a shafinta na Facebook.
Wani jami’in ofishin shugaban kasar ya shaida wa kamfanin dillancin labarai na Anadolu ta wayar tarho cewa har yanzu gwamnati na kan tattara cikakkun bayanai game da “yanayin da ke kara girma.”
Hukumar binciken yanayin kasa ta Amurka (USGS) ta sanar da cewa, wurin da girgizar kasar ta ta auku ya kai nisan kilomita 18 (mil 11) daga kudu da birnin Hualien.
“Baya ga asarar rayuka da barna da aka fuskanta, tasirin iftila’in ba zai wuce (misali) wasu yan wurare ba,’’ in ji hukumar
Ko da yake hukumar kula da yanayi ta Taiwan CWA ta ce girgizar kasar ta kai maki 7.2, tana mai cewa ta afku ne a gabar tekun birnin Hualien da ke gabashin Taiwan da misalin karfe 7:58 na safiyar ranar Laraba (23:58 GMT na ranar Talata).
Wasu faifan bidiyo da kafafen yada labarai na kasar suka fitar sun nuna cewa wasu gine-gine a birnin sun ruguje sakamakon girgizar kasar da ta afku wanda zurfinsa ya kai kilomita 34.8 (mil 21).
Hukumar CWA ta kuma yi gargadin afkuwar mahaukaciyar guguwa mai tafe da ruwan sama ta tsunami a yankunan arewacin tsibirin kasar bayan iftila’in girgizar kasar, wanda ya haddasa zabtarewar kasa.