✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Sojojin Sudan sun kashe mutum 40 suna tsaka da cin kasuwa a Khartoum

An kuma jikkata akalla mutum 70 yayin harin

Sojojin kasar Sudan sun kai wani hari ta hanyar amfani da jirgi mara matuki a kan wata kasuwa da ke garin mayo a dab da birnin Khartoum, inda suka kashe mutum 40.

Ma’aikatan lafiya da masu fafutukar kare hakkin dan Adam ne suka tabbatar da hakan, a daidai lokacin da sojojin da ke mulkin kasar ke ci gaba da yaki da rundunar ’yan tawaye ta RSF.

Harin ya kuma jikkata akalla mutum 70 a ranar Lahadi kamar yadda wasu ma’aikatan lafiya a Asibitin Koyarwa na Jami’ar Bashair, inda aka kwantar da mutanen, suka tabbatar.

Sun kuma ce galibin wadanda aka jikkata din sai sun bukaci a yanke musu kafafu ko hannuwa.

Kungiyar RSF dai ta wallafa wasu hotuna a kafafen sada zumunta na zamani da ke nuna gawarwakin mutanen da aka kashe nannade a cikin farin likkafani a wani fili da ke asibitin.

Wakiliyar gidan talabijin na Aljazeera a Khartoum, Hiba Morgan, ta rawaito cewa sojoji ne suka kai harin.

Sai dai ta ce babu tabbacin ko dukkan wadandan aka hallaka a harin fararen hula ne, amma ya ce, “wadanda aka jikkata na tsananin bukatar agajin lafiya.”

Kai hare-hare ta sama ya zama ruwan dare tun lokacin da aka fara yakin Sudan, lamarin da ya mayar da babban birnin kasar na Khartoum ya koma wani filin daga.

Sai dai wakiliyar gidan talabijin din ta ce babu alamun kawo karshen rikicin a nan kusa sakamakon har yanzu ba a fara tattaunawa ba tsakanin sojojin da dakarun RSF, kimanin wata biyar da fara yakin.