✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Girgizar kasa ta kashe mutane 300 a Kasar Haiti

Girgizar kasar da ta dade tana wanzuwa a mafi akasarin yankin Caribbean.

Girgizar kasa mai karfin maki 7.2 ta afka wa kasar Haiti da safiyar Asabar, inda ta kashe fiye da mutane 300 tare da rusa gine-gine.

Hakan ya faru ne a yayin da kasar ke farfadowa daga makamanciyar musibar girgizar kasar da ta afka mata a shekarar 2010.

Ma’aikatar Binciken Yanayin Kasa ta Amurka ta ce, inda girgizar kasar ta auku na da nisan kilomita kimanin 160 daga tsakiyar Port-au-Prince babban birnin kasar Haiti da ke da cinkoson jama’a.

Haka kuma, ta ce girgizar kasar ta ranar Asabar ta fi tasiri ne a wani wuri mai nisan kilomita 12 da garin Saint-Louis du Sud.

Wata mata, Christella Saint Hilaire da ke zaune kusa da wurin da abin ya faru, ta shaida wa AFP cewa gidaje da makarantu da dama sun rushe, a yayin da gwamman mutane suka jikkata baya ga wadanda suka halaka.

Kafar Watsa Labaran Amurka ta CNN, ta ce an dai ji girgizar kasar da ta dade tana wanzuwa a mafi akasarin yankin Caribbean, inda fiye da mutum 1,800 suka jikkata.

Tuni dai gwamnatin Haiti ta ayyana dokar ta baci don magance bala’in, yayin da kuma wani jami’in Fadar White House ya ce Shugaban Amurka Joe Biden ya ba da umarnin fara ayyukan agaji cikin gaggawa.

Girgizar kasar da ta faru a Haiti a 2010 ta kashe mutum sama da 200,000 tare da haddasa barna mai yawa ga kayayyakin more rayuwa da tattalin arziki.