✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Girgizar ƙasa ta kashe mutum 95 a ƙasar Tibet

Mutum 95 ne suka rasu wasu aƙalla 130 suma jikkata a yayin da gine-gine sama da 1,000 suka lalace sakamakon girgizar ƙasar da ta auku…

Aƙalla mutum 95 ne aka tabbatar sun rasu sakamakon girgizar ƙasa da aka samu a ƙasar Tibet.

Wasu mutum 130 sun jikkata a yayin da gine-gine sanda 1,000 suka lalace a cibiyar Ibtila’in da ke yankin Tingri, a cewar kamfanin dillancin labarai na Xinhua na ƙasar China.

A safiyar Talata ce aka samu girgizar ƙasar mai ƙarfin maki 7.1 da faɗin kilomita 10 a yankin Tingri, inda ta yi sanadin rushewar gine-gine.

Girgizar ƙasar ta kai yankin Himalaya da ke kasar Nepal, ind Dutse mafi tsawo a duniya, Everest yake, da kuma Arwa Indiya da ke makwabtaka da Tibet.

A yayin da ake ci gaba da aikin ceto hukumomi sun dakatar da ayyukan da suka danganci hawa dutsen Everest, hasali ma an rufe sansanin ’yan yawon bude ido da ke shirin hawa dutse.