Yanzu haka akwai mutane tara da suka makale a cikin wani ginin bene da ke ci gaba da nutsewa cikin kasa a unguwar Maryland da ke Jihar Legas.
Wakilinmu ya ruwaito cewa, wannan dai na faruwa ne a sakamakon ruwan saman da aka tafka kamar da bakin warya, lamarin da ya haddasa ambaliyar ruwa a sassan birnin.
- Wata mata ta kashe kanta saboda nauyin bashi
- Sun yi garkuwa da jariri, suna dukan mai jego don a ba su N50m
Hukumar Ba da Agajin Gaggawa ta Kasa NEMA ta ce, ginin na nan a lamba 47, layin Akinwunmi da ke rukunnin gidajen North Estate, Mende a unguwar ta Maryland da ke Ikeja, babban birnin Legas.
Jami’in Hulda da Jama’a a Hukumar ta NEMA, Ibrahim Farinloye ya bayyana cewa, sun samu kiran .waya da ke shaida musu halin da benen ke ciki na ci gaba da shigewa cikin karkashin kasa.
A cewar Farinloye, har yanzu akwai mutane 9 da suka gaza fitowa daga ginin.
Rahotanni na cewa, mamallakin gidan, ya yi amfani da tsani domin tsira da ransa, amma Hukumar NEMA ta tuhume shi saboda yadda ya gaza tumtubar ta, inda daya daga cikin mutanen da suka makale ne ya yi karfin hali har ya kira wayar hukumar.
A halin da ake ciki dai masu ruwa da tsaki da suka hada da jami’an NEMA da na Hukumar Ba da Agajin Gaggawa na Jihar Legas, LASEMA, sun shiga aikin ceto.