✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Gine-Ginen Gidan Sarautar Kano: Jiya da Yau

dan Adam kayan Allah! Ubangiji da Ya halicci mutane, shi kadai Ya iya masu. Abin mamaki ne a ce wani ya koka ko ya kai…

dan Adam kayan Allah! Ubangiji da Ya halicci mutane, shi kadai Ya iya masu. Abin mamaki ne a ce wani ya koka ko ya kai kara game da sauye-sauye da gyare-gyaren gine-gine a gidan sarautar Kano. Ko da yake ina daya daga cikin masu kallon abin a matsayin neman suna ko kuma tunanin da akwai wani lauje a cikin nadi, musamman in aka yi la’akari da lamarin sauye- sauye da gyare-gyare da kare-kare a gidajen sarautun kasar Hausa ba sabon abu ba ne kuma mai martaba Sarki Sanusi II ba shine farau ba.

A bayyane yake, kokarin da sarkin yake na bunkasa masaurautar Kano da kuma yadda yake kara kawata gine-gine da za su kara wa fadar kwarjini a cikin masaurautun kasar Hausa, ba karamin abin alfahari ba ne gare mu baki daya kuma ba wai shi ne na farko da ya aiwatar da gine-gine ko gyare-gyare a masarautar Kano ba. Wannan abu ne da ya gada daga kaka da kakanninsa, sai dai a ce kowane zamani yana tafiya da mutanensa.
Kasancewar sarki a matsayin kwararre kuma daya daga cikin jerin shahararrun mutane dari na duniya kamar yadda babbar mujallar nan mai fada a ji, wato Times ta tabbatar, ba na tunanin zai yi koyi da abin da bai dace ba a kokarinsa na kyautata gine-ginen fadar Kano, sai dai zai inganta masarautar a matsayin ginin zamani amma tare da kwalliyar gargajiyarmu ta Hausa.

Duk da kasancewar Gidan Sarki daya daga cikin gidajen tarihi, bai kasance gidan ajiyar kayan tarihi ba, ko don kasancewarsa mutane ne ke zaune a ciki ba kaya ba. Za a iya samar da gyara ko don jin dadin zama a waje ko don kawata masarauta ko kuma don zamanantaka ko don mayar da wani gini da ya rushe.
Bisa al’adun masaurautun kasar Hausa, kowace masarauta tana da irin nata gine-ginen, wadanda ta gada daga asalin wadanda suka kafa wannan masaurauta. Misali, tun daga lokacin jihadin Shehu danfodiyo, bayan kafa daular mulkin Fulani a kasar Hausa aka raba wa sarakuna tuta irinsu. Sarakuna irin su Sarki Suleimanu wanda ya mulki kasar Kano 1805 zuwa 1819 Sarki na 40 a sarakunan Kano kuma na farko a sarakunan Fulani. Ummarun Dallaje, Sarki na 39 a cikin sarakunan Katsina, kuma na farko cikin sarakunan Fulani. Bauchi Yakubu, Gombe Buba Yero da sauran jihohin kasar Hausa, kowane sarki da tasa tutar da Shehu danfodiyo ya ba shi, sai ya koma ya gina shigifa ya sanya tutarsa a sama. Wannan shi ne asalin soron tuta da yanzu ake gani a akasarin gidajen sarautarmu.
Duk kusan gaba daya masaurautun, tun daga Sakkwato zuwa Gombe da Adamawa da Katsina da Bauchi, daga wacce aka rushe aka sake ginawa sai wacce aka kara wadansu gine-ginen tare da yi musu ado da kwalliya da makuba ko zanen zayyanar dada kyau don sake kawata su.

Kano babbar kasa ce kuma masarauta ce mai kwarjini a cikin kasashen Hausa da kewaye. Kuma masarauta ce wacce manyan sarakuna masu kasaita suka mulke ta, tarihi ya nuna sarakuna irinsu; Bagauda (999-1063), Warisi (1063-1095), Gijimasu (1095-1134), Nawata (1134-1136), Yusa (1136-1194), Naguji (1194-1247), Guguwa (1247-1290), Shekarau (1290-1307), Tsamiya (1307-1343), Usman Zamna Gawa (1343-1349), Yaji I (1349-1385 da sauransu.
An ruwaito cewa Sarkin Kano Muhammadu Rumfa na cikin manyan sarakunan da suka fara rugujewa da gyara da kuma yin sababbin gine-gine a gidan sarautar Kano. Tarihi ya nuna lokacinsa ne aka gina shigifofi da dama a gidan sarautar Kano don killace matan Sarki a matsayinsa na mai kishin addini.
Zamanin Sarkin Kano Ibrahim Dabo, shi ya samar da gini na fadar Kano wacce aka yi mata ado da yunbu. Ita wannan fada shigifa ce mai matsakaicin girma kuma an yi mata shinge daga cikinta.
Sarkin Kano Abdullahi Maje Karofi, da na biyu wajen Sarki Ibrahim Dabo (1855-1883); shi ma ya gina shigifa da kuma sake gina kofar fatalwa a cikin masarautar Kano.
Zamanin Sarkin Kano Muhammad Bello (1883-1893), da na uku wajen Sarki Ibrahim Dabo wanda Sarkin Musulmi Umar dan Aliyu ya nada. An ce shi ne a zamaninsa ya gina shigifar da ake kira Soron Bello da kuma wasu shigifofi guda biyu na zaman sarki a gidan sarautar Kano.
Sarkin Kano Muhammadu Tukur (1893-1894) wanda Sarkin Musulmi Abdurrahaman ya nada. dan Sarkin Kano Muhammadu Bello ne shi kuma ya yi Galadiman Kano kafin ya zamo sarki. A lokacinsa tarihi ya nuna an kara yawan soraye, daya daga ciki makarantar allo ce inda ake ce wa Soron Makaranta, ya yi shigifofi kuma domin ajiyar makaman yaki don a lokacinsa ne aka yi yakin basasa.
Sarkin Kano Aliyu Babba (Alu mai Sango), dan Sarkin Kano Maje Karofi, dan Saudatu ’yar Sarkin Musulmi Aliyu Babba, dan Sarkin Musulmi Bello (1894-1903). Tarihi ya nuna a zamaninsa ya gyara masallacin gidan Sarki ya kuma gyara wasu soraye guda biyu da suka rushe. A wani kaulin ma ana cewa Sarki Alu ne ya katange gidan sarautar Kano gaba daya daga kofar Kudu har zuwa kofar Fatalwa.
Sai kuma Sarkin Kano Muhammad Abbas dan Sarkin Kano Maje Karofi (1903-1919). Ya yi Sarkin Dawakin tsakar gida kuma ya yi Wambai kafin zamansa Sarki. Shi ne Sarki na farko da Turawa suka rantsar a gadon mulkin Kano. Tarihi ya nuna zamaninsa an yi wa gidan sarautar Kano yabe da makuba kuma an yi wata kwalliya da zanen tambarin sarauta a jikin garu.
Zamanin Sarkin Kano Alhaji Abdullahi Bayero dan Sarkin Kano Muhammadu Abbas (1926-1953) wanda ya yi Ciroman Kano kafin zamansa Sarki, kuma shi ne Sarki na farko da ya fara zuwa aikin Hajji, a zamanin da yake kan gadon mulkin sarautar Kano. Ya gudanar da mulki ne karkashin Turawan mulkin mallaka, amma duk da haka Sarki Alhaji ya rushe babban masallaci, ya gina babban masallacin juma’a na Kano, wanda a lokacin ginin kasa ne, shi ne ya sake gina shi kamar yadda yake a yanzu. Har ila yau, ya sake gina wasu soraye da bukkoki na kwanciyar bayi kuma ya sake wasu rufin dakuna da suka yaye lokacin damina, wasu kuma sun ce lokacinsa ya maida hankali sosai wajen yin ayyukan jin dadin talakawansa da bayinsa. Tun daga muhalli zuwa sutura da abinci a zamaninsa bayin Sarki sun samu kulawa.
Sarkin Kano Sir, Khalifa Muhammadu Sanusi I, babban dan Sarkin Kano Alhaji Abdullahi Bayero (1953-1963). Ya yi Ciroman Kano kafin zamansa Sarkin Kano. Ya fara gudanar da mulki karkashin Turawan mulkin mallaka, a zamaninsa ne kuma Najeriya ta samu ’yancin kai a 1960 daga hannun Turawan mulki. A zamaninsa, shi sarki ne mai kwarjini da muhibba da kuma fada a ji. Tarihi ya nuna an yi wata gobara a wajen bukkokin bayi a lokacin da ake yin alewar madi. Dalilin wannan gobara sarki ya sanya duk aka rushe bukkokin gidan masarautar Kano, aka yi ginin kasa mai kyau, aka yi rufin azara. An yi gyaran katanga tare da gina soraye na alfarma; ciki kuwa har da soron Ingila wanda aka gina domin zuwan sarauniyar Ingila, wacce ta ziyarci masarautar Kano a 1956.
Ayyukan da Sarki Muhammadu Sanusi I ya yi a bangaren ilimin zamani ma, Abdulrahman Sarkin Kotso ya bayyana su a wakar ‘Mamman Zakin Daga na Abashe.’
“Zamanin dan Audu nikatau
Birnin Kano ko ana an karu
Ga makarantu an yi fiyayyu
Ga siniya sakandare na nan
Furobishal sakandare na nan
Ga siniya firamare na nan
Ga makarantun mata na nan
Iliminmu yau ya kai ga kwaleji
Ga Bayero Kwaleji tana nan
Makaranta babba a Nauzan
Duk a kasashe babu irinta
Sai Kano garin Mamman na Abashe
Sa Sanusi sarkin yaki, zakin daga na Abashe.”
Za mu ci gaba